Buhari zai tafi turai yau Talata:

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Belgium a yau Talata don halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar haɗin kan Afirka ta African Union (AU) da takwararta ta Tarayyar Turai (EU).

Taron wanda zai gudana a birnin Brussels daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta ce ana sa ran Buhari zai koma gida ranar Asabar. Ta ƙara da cewa shugaban zai yi amfani da damar wajen tattauna sauran al’amura da wasu ƙasashe.

Abubuwan da shugabannin za su tattauna sun haɗa da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.

Dole ne musulmi da kiristoci su Hada kansu~~ sardaunan matasan karu:

Daga Aliyu Muhammad~kaduna

Sardaunan matasan karu. L. G .A kuma katukan maraba Alhaji Amadu Ibrahim yayi kira ga matasan kiristoci da na musalmai a yau ranar haihuwar Annabi isa.

Alhaji Amadu Ibrahim sardaunan matasan katu kuma katukan maraba yaja hankalin Al’ummar kirisoci dana musulmai a yau Asabar 25/12/2021 a lokacin da muka tattauna da shi domin taya kiristoci murnar kirsimeti.

katukan yaja hankalin shuwagabanni da sarakunan gargajiya da su kasance masu Adalci ga Al-ummar da suke jagoranta.

mai sarautar matasan yayi kira ga pastoci da malaman Addini da su zama wakilan Annabawa a duk inda suke, ta hanyar yiwa mabiyan su huɗuba ta gari.

katukan marabar yaci gaba da cewa a wannan yanayi da kasar ta tsinci kanta na rashin ingantaccen tsoro dolene kowa ya zama ya tsarkake zuciyarsa domin mu ceto kasarmu Nigeria daga halin data tsinci kanta.

sannan yaci gaba da cewa matasa sune kashin bayan Al-umma domin kuwa duk wani Abu da kagani da matasa Ake yinsa, domin haka kuwa wajibin shuwagabanni ne su jawo matasa a duk wani Al a muran su wajen samarwa matasan Aiyukan yi.

Daga karshe Alhaji Amadu Ibrahim Adu’a yayi ga shugaba Buhari da Allah ya karamasa lafiya ya kuma bashi ikon jagorantar mutane da Adalci.

Yankin Arewacin Nigeria Yana cikin Matsanancin Rikici: El-rufa’i

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce yankin arewa maso yamma na kasar nan ya na cikin matsanancin rikici

Gwamnan ya kwatanta halin da yankin ya fada da yanayin halin da kasar Afghanistan ta fada na rikici

Ya bayyana yadda rashin tsaro ya ke shafar fannonin da suka hada da ilimi da kuma lafiya, lamarin da ke kara tada hankali

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na tangal-tangal – Inji Salomon Dalung

Daga Dallami Birnin Gwari.

Dalung ya fadi hakan ne a hirarsa da BBC Hausa

Jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Mista Solomon Dalung, wanda tsohon minista ne a gwamnatin, ya ce APC ta gaza wajen cika alkawuran da ta yi wa ƴan ƙasar.

Mista Dalung ya shaida hakan a hirar da BBC ta yi da shi ya ce batun inganta tsaro shi ne babban alkawarin da jam’iyyar ta yi wa ƴan Najeriya, amma yadda tsaro ya tabarbare, musamman ma a arewacin ƙasar, APC ba ta da kyakkyawar makoma, kuma ba ta da idon da za ta kalli jama’ar kasar da shi.

Ya ce matsalar ta tsaro ta jefa rayuwar jama’a cikin zulumi da tsoro saboda yin tafiya cikin Arewa a halin da ake ciki ta zama tashin hankali saboda dole ne sai mutane sun haɗa da addu’a da kuma azumi.

“A ce wai a Arewa wai kafin ka yi noma sai ka biya ɗan bindiga kuɗi, idan ka gama noman ka biya shi kuɗi kafin ka zo ka yi girbi, ina ma ke nan maganan noma a Arewa?”, in ji tsohon ministan.

A ganinsa, ba a taɓa shiga irin wannan yanayi ba saboda “gwamnatin nan da muka kafa, ba ta biya wa ƴan Najeriya buƙata ba, gwamnatinmu ce amma yanzu idan ba mu yi dai-dai ba, haƙƙinmu ne mu fita mu faɗa domin mun yi wa wasu jiya, saboda haka sai mu yi wa kanmu yau”.

Jam’iyyar APC na cikin garari….

A cewar Solomon Dalung, APC ba ta da wata makoma saboda “a yanzu an rushe jam’iyyar baki ɗaya, ba ta da mambobi – ko shugaban ƙasa ma ba mamba bane”.

Ya ce “mu yanzu ma ba ƴan APC bane, sai an dawo mana da takarda mun sake shiga jam’iyya kamar shigar soja”.

Tsohon ministan ya soki matakin kafa kwamatocin riƙo inda ya ce “ba za ka tashi yau saboda gidanka na yoyo ka kawo katafila ka rushe gidan a koma a yi sabon gini”.

A halin yanzu, ya ce shi tsohon ɗan APC ne domin yana jira ne a sake buɗe ƙofa sai ya shiga.

Mataimakin tsohon Gwamna Yari ya Canza Sheka zuwa PDP: 


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Mataimakin tsohon gwamnan jihar Zamfara,Hon Abdulaziz Yari ,Malam Ibrahim Wakala Liman yayi kaura Daga jamiyya mai mulkin kasar wato APC inda ya koma jam’iya mai mulkin jihar zamfara PDP tsohon mataimakin Gwamnan na zamfara Alhaji ibrahim wakkala ya kwashe tsawon shekaru takwas yana Mataimakin gwamna a karkahin  jamiyyar  ta APC a jihar ta Zamfara.
Malam  Wakala ya tabbatar da hakane a Wani  taron manema labarai da gabatar a gidansa da ke Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.
Wakala Liman ya bayyana cewa,”dalilansa na canza shekar kamar haka,”Bani da jihar da ta wuce jihar Zamfara, kuma duk wanda yake da kudirin cigaban Zamfara, ya zama wajibi mu maramasa baya.
“Ganin yadda gwamnatin jamiyyar PDP ta ke taka rawar gani  wajan cigaban jihar ta kowane sashe, kuma gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun yana amsar shawarwari na domin   ci gaban jihar, shine ya karamanin kwarin guiwa na canza sheka zuwa ga Jamiyyar PDP.” inji Malam Wakala.
Masu iya magana na cewa,” Zara bata barin dami,yanzun haka jamiyyar PDP,mai mulikin jihar Zamfara na yiwa jamiyyar adawa ta APC dauki daidai a jihar ta zamfara.
Dan a makon da ya gabata ne mebawa tsohon gwamna Yari shawara a Bangaren yada labarai da Sadarwa,Ibrahim Muhammad Dosa, shima ya canza shekarzuwa Jamiyyar PDP mai mulkin jihar  Zamfara.

Jihar Nasarawa ta lashe Gasar Damben da Aka fafata na jihohi 7 a jihar kano:

‘Yan wasan Dambe da suka wakilci jihar Nasarawa sune suka lashe gasar Damben kasa na jihohi 7 a jihar kano.

Wannan gasa an farata ne a jihar katsina daga bisani aka zagaya jihar Nasarawa da kuma jihar Niger ranar juma’a kuma aka 27-11-2020 aka sake Bugawa a jihar ta kano inda wasan ya Dsuki kwanaki uku anayi.

Idris Bambarewa dai daga jihar Nasarawa shine ya jagoranci ‘yan wasan na jihar an fafata wasan na karshene da jihar Niger da jihar Nasarawa.

Gwamnatin jihar sakkwato Zata Kafa hukumar Hisbah:

Daga shehu yahaya sokoto


Gwamnatin jihar Sakkwato ta Kammala shirinta na kafa hukumar Hisba ta jihar domin ganin an Kara samar yanayi mai kyau na Kula da tarbiyyar al’ummar jihar bisa tsari dokokin addinin Islama.
Bayan haka ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar Laura addinin musulunci ta jihar Hon. Abdullahi Maigwandu, a Wata zantawa da yayi da manema a labari.
Kwamishinan yace tuni kwamitin da gwamnan ya kafa akan tsara yadda hukumar zata kasance ya miki rahotonsa
Hon. Abdullahi Maigwandu, ya ci gaba cewa “Maigirma gwamna Aminu Kairi Tambuwal ya karbi rahoton Kwamitin daya kafa akan aikin Hisba a jihar karkashin jagorancin maigirma Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali Junaidu tare da mambobin wannan kwamitin wadanda suka hada da wakilan ja’mian tsaro daga kowane bangare”
“Akwai Manyan Malaman addini da sauran su Wanda Sun gabatar da rahoton wannan kwamitin ga maigirma gwamna a fadar gwamnatin jihar” inji shi.
Idan aka kafa hukumar ta hisba zata kasance karkashin kulawar ma’aikatar lamuran Addinin musulunci ta jihar .

Kwamishinan ya kuma bada tabbacin cewa Nan bada jimawa ba gwamnati zatayi duba tare da aiwatar akan rahoroton na kafa hukumar Hizba a jihar domin kara ingantuwar aikinta.

Yayin karbar wannan rahoton gwamna Tambuwal ya bayyana jin dadin sa tare da yabawa ga dukkanin ‘yan wannan kwamitin bisa hazaka da kokarin da sukayi na sauke nauyin da gwamnati ta Dora masu domin samar da hanyar da za’a inganta aikin Hizba a jihar Sakkwato.

Damben Dubu Dari Biyar waye Gonin ka Gobe 29-11-2020 a Marabar Nyanay.

Gagarumin Damben Naira 500,000 Dubu Dari Biyar Gobe lahadi 29-11-2020 na kwamishinan wasanni na jihar Nasarawa Alhaji usman Boss da Sardaunan matasan maraba kuma katukan Maraba na farko Alhaji Amadu Ibrahim ‘yan kallo karku bari kallo ya barku kudin shiga Naira dari biyar 500 https://youtu.be/UD2StePDfd4

Mugun Damben Gargajiya yau juma’a 27-11-2020 a Marabar Nyanya ta jihar Nasarawa:


Yau juma’a 27-11-2020 mun leka gidan Damben Bambarewa da yake Marabar Nyanya ta jihar Nasarawa inda matasa suka fafata Dambe har hawa uku Damben farko Anyi Dambe tsakanin shagon Bahagon  Ali yaro na Gurumada da shagon Inda bangaren Arewa sunyi turmi uku Babu kisa.


Sai Dambe na biyu tsakanin shagon Bahagon Dogon Auta na Bangaren kudu da shagon tanko na gurumada suma sunyi kazamin Dambe turmi uka babu kisa.


Dambe na karshe shine na uku tsakanin Dan filanin Bahagon sani maimaciji na bangaren kudu da shagon Autan Bagaye na Arewa.
Masu sha’awar wasannin Damben Gargajiya sai ku rinka binmu a shafinmu na facebook ko shafinmu instagram Hausa online tv ko kuma a shafinmu na 

Design a site like this with WordPress.com
Get started